Yayin tattaunawa da manema labarai, ministan ilimi na ƙasar Saleh Mamman yace tuni gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarabawar ta WAEC da ta tabbatar da bibiyar shaidar haihuwar ɗalibai kafin basu damar rubuta jarabawar a duk shekara.
A cewar Salleh Mamman wannan dai ba wata sabuwar doka ce aka bijiro da ita ba, dama akwaita kawai dai a wannan lokaci za’a tabbatar da cewa tana aiki yadda ya dace.
Ministan ya kuma ƙara da cewa ko da rubuta jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB itama tana ƙarƙashin wannan doka ta cewa dole sai dalibi ya kai shekara 18 kafin ya sami damar rubutawa.
Da yake mayar da martani kan matakin gwamnati na korar ma’aikata kusan dubu 23 daga bakin aiki saboda mallakar shaidar kammala karatu daga jami’o’in Togo da kuma Jamhuriyar Benin, ministan yace a yanzu gwamnatin tarayya jami’o’i 8 kaɗai ta sahalewa su baiwa daliban Najeriya sakamakon kammala makaranta a ƙasashen biyu.
Ya kuma ce cikin jami’o’i 8 din uku na Togo sai guda biyar daga jamhuriyar Benin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI