A jawabin da ya gabatar gaban manema labarai bayan halartar taron majalisar tattalin arziƙi da ya gudana a fadar shugaban ƙasa ta Villa da ke Abuja, Mr Edun ya ce bashin ne kaɗai hanyar da Najeriya za ta iya magance matsalar ta giɓin kasafin kuɗi a wannan karon.
Jumular kuɗin gudanar da ayyuka da ke cikin kasafin ya kai naira tiriliyan 34 da biliyan 8 daga cikin ƙunshin kasafin na naira tiriliyan 47 da biliyan 9 wanda ke nuna ƙaruwar kashi 36.8 daga kasafin 2024.
Jumullar giɓin da ke ƙunshe a kasafin na bana na matsayin naira tiriliyan 13 da biliyan guda wato kashi 3.39 na ma’aunin tattalin arziƙi na GDP.
A cewar Mr Edun an gudanar da kasafin kuɗin na baɗi ne bisa ga duba ga irin gagarumin ci gaban da ƙasar ta samu ƙarkashin jagorancin watanni 18 da shugaba Tinubu ya shafe a kan kujerar mulkin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI