Najeriya za ta fara killace fasinjan da suka shiga ƙasar daga China

Najeriya za ta fara killace fasinjan da suka shiga ƙasar daga China

Bayanai sun ce tuni wannan cuta ta haddasa cunkoso a asibitocin China ta yadda jami’an lafiya ke ci gaba da bayar da kulawar gaggawa baya ga kulle wasu sassa na ƙasar.

Cutar wadda ke da alaƙa da lumfashi, bayanan da ƙwararru suka bayar sun ce tafi harbar ƙananan yara kuma ta kan yaɗu daga mutum zuwa mutum, batun da tuni ya tayar da hankalin jama’a.

Tuni dai aka ga ɓullar wannan cuta a wasu ƙasashen wanda ya sanya tsaurara matakai don kaucewa yaɗuwarta a sassan maƙwabtan Chinar da suka ƙunshi Cambodia da Taiwan da kuma Hong Kong.

Mahukuntan China sun ce a ƴan kwanakin nan ana ganin ƙaruwar yaran da ke harbuwa da cutar galibi ƴan shekaru 14 zuwa ƙasa musamman a yankin arewacin kasar.

Wannan sabuwar annoba na zuwa a dai dai lokacin da ake cika shekaru 5 da ɓullar cutar Covid-19 a yankin Wuhan na tsakiyar ƙasar, cutar da ta harbi mutane miliyan 777 baya ga kisan wasu fiye da miliyan 7 a ƙasashe daban-daban na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)