
Ministan lafiya da walwalar jama'a na Najeriya, Muhammad Pate, ya bayyana hakan, yayin hira da wata kafar talabijin na ƙasar a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin shigar da ma'aikatan cikin tsarin kiwon lafiyar ƙasar tare da rage dogaro da tallafi da ƙasashen ƙetare ke bayarwa.
Mista Pate ya bayyana gagarumar gudunmawar da gwamnatin Amurka ke bayarwa a fannin kiwon lafiyar Najeriya, musamman a bangaren cutar kanjamau, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, sai dai ya jaddada cewa Najeriya ta kuduri aniyar daukar nauyin sashen kula da lafiyarta da kuma rage dogaro da tallafin da take samu daga waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI