Babban mashawarcin shugaban ƙasar kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribado ne ya bayyana hakan yayin wani taron kwanaki biyu game da batun sauyin yanayi da ke tasiri kan tsarin mallakar makamai da bazuwar su a hannun farar hula ba bisa ƙa’ida ba.
Yayin taron da aka gudanar a birnin Abuja, Nuhu Ribado ya ce Najeriya a hukumance ta gano wasu alamu da ke tabbatar da cewa mashigin tekun Guinea na zama wata babbar cibiyar kwararar manya da ƙananan makamai a hannun jama’a a Najeriya.
Taron wanda cibiyar kula da kuma daƙile yaɗuwar ƙananan makamai a hannun fararen hula ta shirya na da nufin gano hanyoyin da za’a bi wajen rage hanyoyin da ƴan ta’adda ke samun makamai a Najeriya.
Malam Ribadu wanda ya sami wakilcin daraktan harkokin waje na ofishin mashawarcin tsaron ƙasar Ibrahim Babani ya kuma ƙara da cewa mafi yawancin masu shigar da makamai Najeriyar ta wannan hanya, na fakewa da irin tarin albarkatun da ke jibge a wannan yankin.
Ƙasashe akalla 16 ne ke kewaye da wannan mashigi na Guinea cikin su kuma har da Najeriya da ke da aƙalla Kilomita 6,000, amma kuma a yanzu wannan mashigi na neman zama barzana ta fannin tsaro a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI