Najeriya: Uwa da yaranta 5 sun mutu bayan cin ɗan wake a Kano

Wasu majiyoyi sun bayyana yiwuwar shigar tsaka cikin garin ɗan waken da aka dafa wanda ya haddasa ajalin mutanen 6 nan ta ke.

Wani ganau daga garin da wannan ibtila’i ya faru wanda ya bayyana sunansa da Garba Muhammad ya bayyana cewa, yanayin rayuwa ne ya tilasta Uwar yaran ɗakko wani ajiyayyen garin rogo don yin ɗan waken da shi ba tare da sanin zai zama ajalinta da iyalinta baki daya ba.

Mahaifiyar wadda ke rike da marayu 6 da tuni mahaifinsu ya rasa ransa, na sahun mabuƙatan da ke fama da rayuwa a jihar ta Kano mai ɗauke da tarin masu ƙarafin ƙarfi waɗanda abinci ke yiwa wuyar samu musamman a halin da ƙasar ke ciki.

Rahotanni sun ce jim kaɗan bayan da ahalin suka kammala cin ɗan waken ne suka fara ciwon ciki kuma a ƙanƙanin lokaci suka rasa rayukansu baki ɗaya.

An dai bayyana sunayen waɗanda suka rasa rayukan na su da Alhakatu Abdulkarim wadda ita ce mahaifiyar sai yaranta 5 da suka kunshi Bashir Abdulkarim da Firdausi Abdulkarim sai Hafsat Abdulkarim baya ga Usman Abdulkarim da kuma Jamilu Abdulkarim.

Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakkinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce suna ci gaba da bincike akan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)