Najeriya: Tinubu ya nuna alhininsa kan mutuwar ƴara a turmutsitsin Ibadan

Najeriya: Tinubu ya nuna alhininsa kan mutuwar ƴara a turmutsitsin Ibadan

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar jiya Alhamis, ta ce ta kuma kama mutane takwas dake da alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsitin na ranar Laraba, ciki har da tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Agunwusi.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa, gidauniyar Wings da kuma abokan huldar su gidan radiyon Agidigbo FM ne suka shirya bukin, ba tare da wani izini da ya dace ba, ko kuma matakan kariya.

Tinubu ya bukaci gudanar da bincike kan turmutsitsin Ibadan

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a turmutsitsin na birnin Ibadan.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban ma’aikatan gwamnan Oyo, Mista Segun Ogunwuyi, ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai 40.

A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai ya fitar, shugaban ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Oyo da kuma musamman iyalai da suka rasa ƴaƴansu a wannan lamari mai cike da takaici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)