Najeriya ta zargi kamfanin China da yunƙurin ƙwace mata jirage da kadarori

Najeriya ta zargi kamfanin China da yunƙurin ƙwace mata jirage da kadarori

A baya bayan nan ne rahotanni suka ce baya ga jiragen alfarmar uku na fadar gwamnatin Najeriyar, tuni kamfanin na China ya fara ƙokarin neman ƙarin izinin kotuna, domin ƙwace wasu kadarorin Najeriyar a ƙasashen Amurka da Birtaniya, da Canada, da Belgium,sai Singapore, da tsibirin Viergin da kuma Faransa.

Sai dai bayanai sun ce a halin yanzu kamfanin na China ya saki ɗaya daga cikin jiragen alfarmar gwamnatin Najeriyar uku da a baya ya tsare.

A shekarar 2001, Najeriya da China suka ƙulla yarjejeniyar zuba hannayen jari ta ban gishiri in baka manda. Bayan haka ne kuma a shekarar 2007, gwamnatin jihar Ogun a Najeriyar, ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Guangdong dake hada-hadar kasuwanci, domin gina masana’antu da kuma katafaren wurin shaƙatawa, sai da a 2016, yarjejeniyar ta rushe, lamarin da ya sa kamfanin rugawa kotu domin neman hakkinsa na yarjejeniyar kasuwancin.

Haka dai shari’a ta ci gaba da gudana har zuwa wajen Najeriya, inda daga ƙarshe wata kotu a Paris ta hana Najeriya amfani ko kuma sayar da jiragen alfarmar da gwamnati ta mallaka, har sai gwamnatin jihar Ogun ta biya kamfanin Chinar dala miliyan 74 da dubu 500 a matsayin diyyar soke yarjejeniyar da suka ƙulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)