Shugaban hukumar ta NPC Alhaji Nasir Isa Kwara da ke sanar da wannan alƙaluma yayin jawabinsa gaban manema labarai bayan ziyarar da mai ɗakin shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu ta kai tare karrama jaririn farko da aka haifa cikin shekarar nan a asibitin Asokoro da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, ya bayyana cewa ana samun karbuwar yiwa jarirai rijista a sassan Najeriya.
Shugaban wanda ya samu wakilcin kwamishinan ayyuka na hukumar daga jihar Katsina ya bayyana cewa NPC na aiki tuƙuru wajen ganin kowanne jariri ya samu rijistar haihuwa da zarar an haife shi a ko’ina ya ke a sassan Najeriyar.
Wasu mata da suka kai yaransu allurar rigakafi. AP - Ben CurtisMr Bala Banya ya yi bayanin cewa shirin rijistar jarirai sabbin haihuwa ya sake samun karɓuwa ne bayan haɗin gwaiwar da hukumar ta yi da asibitocin kula da lafiya a matakin farko, baya ga sabunta tsarin rijistar zuwa na zamani saɓanin yadda ya ke a baya.
A cewar jami’in yaran fiye da miliyan 10 da aka yiwa rijistar cikin watanni 3 da suka gabata sun ƙunshi sabbin haihuwa da kuma ƙananun yara ƴan ƙasa da shekaru 5 waɗanda ba a yiwa rijista a lokacin haihuwarsu ba.
Sai dai jami’in na NPC ya bayyana cewa a yanzu sun fi mayar da hankali kan yara ƴan ƙasa da shekaru 5 da ba a samu damar yi musu rijista ba.
Tun kafin yanzu babban daraktan hukumar ta NPC Dr Telson Osifo Ojogun ya sanar da cewa shirye-shirye sun kammala wajen samar da cibiyoyin rijistar jarirai sabbin haihuwa fiye da dubu 4 a sassan ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI