Yayin wani zaman shari’ar mayaƙan boko haram da sauran masu alaƙa da ƙungiyar wanda cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Najeriya da ke ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro ta gudanar a jiya ne aka yi wannan hukunci.
Yayin zaman na jiya da ya ƙunshi ko dai mayaƙan na Boko Haram ko waɗanda suka yi alaƙa da ƙungiyar ko kuma waɗanda ake zargi da kasancewa, bayanai sun ce ɗimbin fursunoni ne suka san makomarsu a jiyan galibinsu waɗanda suka shafe tsawon shekaru ba tare da anyi musu shari’a ba.
A zaman shari’ar wadda aka kasa zuwa rukunnai 6, aƙalla mutane dubu 1 da 743 ne suka gurfana inda a zaman na jiya aka bankaɗo wasu mutane 200 da ake kame waɗanda hujjoji suka tabbatar da alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci.
Bayanai sun ce a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024 mai shirin ƙarewa, mutane 742 aka yankewa hukunci, yayin da da kotu ta wanke 888, sai kuma mutane 92 da aka ɗage shari’arsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI