An bayyana hakan ne a wajen bikin bayar da lambar yabo ta shirin Kafa ƙananan tashoshin samar da hasken lantarkin na Afrika wanda ya gudana a Abuja fadar gwamnatin ƙasar ranar Juma’a.
Taron dai a hukumance ya tabbatar da kaddamar da shirin na samar da sabbin kananan tashoshin guda 23 a yankuna shida na Najeriya.
Wadannan kananan cibiyoyin, masu karfin aiki daga 30 kWp zuwa 200 kWp, an tsara su ne don inganta samar da wutar lantarki a yankunan karkarar da ba a iya amfani da su ba, da ɓullo da wata hanya da zata taimaka wajen samar da makamashi mai dorewa da kuma inganta rayuwa ga ɗumbin 'yan Najeriya.
Wata sanarwa da Cibiyar Muhalli ta Duniya ta fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa, shirin wanda ya fara aiki a kasashe 21 a shekarar 2022, Cibiyar ce ke daukar nauyin shirin da kuma tallafawar shirin raya ƙasashe na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI