Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 13 a ƙoƙarin bai wa Naira kariya- rahoto

Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 13 a ƙoƙarin bai wa Naira kariya- rahoto

Rahoton Bankin duniyar a jiya Laraba ya bayyana cewa matakan zuba maƙuden kuɗi da mahukuntan Najeriyar ke yi ya taimaka wajen kange hauhawar kuɗaɗen ƙetare kan Nairar wadda ke ganin mummunan koma baya.

Bankin Duniyar yayi ƙarin hasken cewa, a shekarar 2021, naira Tiriliyan biyu Najeriyar ta rasa a koƙarin bai wa takardar kudin ƙasar kariya, sai kuma ƙarin Naira Tiriliyan 6.2 a shekarar 2022.

Rahoton Bankin duniyar ya ci gaba da cewa ko a shekarar 2023 da ta gabata, Najeriyar ta zuba tsabar kuɗi har naira Tiriliyan 5 da sunan bai wa takardar kuɗin ƙasar kariya, duk da cewa har yanzu darajar nairar na ci gaba da ganin koma baya.

Wasu bayanai na daban na nuna yadda takardar kuɗin Najeriyar ta Naira ke ganin mafi munin koma baya a wannan shekara yayinda takardun kuɗaden ƙasashen ƙetare ke ci gaba da hawa kan Nairar kama daga Fan na Birtaniya da Yuro na Turai da kuma dalar Amurka, har ma kuɗaɗen maƙwabtan ƙasar irin CFA daga Nijar da Cedi na Ghana da ma kuɗaɗen ƙasashen Larabawa har da Yuan ko kuma RBM daga China.

Ko a baya-bayan zarge-zarge sun yawaita game da yadda mahukuntan Najeriyar ke amfani kuɗaɗen da ke asusun ajiyar ƙasar na ƙetare wajen bai wa Nairar kariya, ko da ya ke mahukuntan sun musunta.

Masana na ganin akwai buƙatar Najeriyar ta ɗauki matakai na gaske wajen dawo da martabar takardar ta Naira wadda babban bankin ƙasar CBN ya karya darajarta a lokuta da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)