
Alkaluman ya nuna saurin habakar bukatun kayyyakin Malta, wanda ya sa ta zama ƙasa ta biyar mafi girma da Najeriya ke shigo da kayayyaki daga garesu a wannan lokacin, wanda ya kai kashi 5.23 cikin 100 na jummalar kayayyakin da ake shigowa da su kasar, da ƙudinsu ya kai N14.67tn.
Sai dai rahoton na NBS bai fayyace ainihin kayayyakin da ake shigo da su daga Malta ba, saidai ya tayar da kura bayan kan zargin da Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote Industries Limited ya yi cewa kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL nada matatar mai a Malta wata karamar ƙasar ta Kudancin Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI