Tukwicin da rundunar ƴan snadan Najeriyar ta sanya da ya kai Naira miliyan 20 za ta bawa duk wanda ya taimaka mata ne wurin kama dan ƙasar mai suna Lucky Obiyan da wani dan Birtaniya Andrew Wynne, da ake zargi da shirya yadda za a kifar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Rundunar ta ayyana mutanen 2 a matsayin waɗanda take nema ruwa a jalllo, saboda shirinsu na kifar da gwamnatin Dimukuradiyya.
A lokacin da yake jawabi ga ƴan jarida mai magana da yawun rundunar yan sandan ƙasar Muyiwa Adejobi, ya ce ana zargin dan ƙasar ta Birtaniya da kitsa yadda za a kifar da gwamnati tare da jefa Najeriya cikin rudani.
Adejobi ya kuma zargi dan ƙasar ta Birtaniya da kama hayar wuri a shalkwatar kwadago ta Najeriya, inda ya ƙirkiri makaranta domin yin basaja a ayyukan da yake shiryawa.
Rundunar ƴan sandan Najeriyar ta ce Wynne ya zuba maƙudan kudi tare da wasu abokananshi ƴan Najeriya, domin su mamaye ofisoshin ƴan sanda da kuma barukokin soji da haddasa zubar da jini, wanda zai sa ƙasashen waje suyi Allah wadai da gwamnatin Najeriya
Rundunar ƴan sandan ta ce tuni wanda suke zargi ya tsere daga Najeriya don haka suka sanya kyautar miliyan goma goma kan kowanne mutum ga duk wanda ya taimaka ka kamasu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI