Ministan Kuɗi gami da tsara tattalin arziƙin Najeriya Wale Edun ne ya bayyana kafa Asusun, yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke birnin Abuja, inda ya ce matakin dole ne lura da cewar matakan kariya ba sa iya hana aukuwar bala’o’i irin su ambaliya, saboda matsalar Sauyin Yanayi.
Miliyoyin mutane ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihohin Najeriya aƙalla 29 inda wasu mutanen kusan 300 suka rasa rayukansu a shekarar bana.
Latsa alamar sauti don sauraron rahoton Nura Ado Suleiman:
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI