A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na intanet, hukumar dake kula da babban layin wutar lantarki a Najeriya, TCN ta ce layin ya sake daukewa da misalin karfe 2 da minti tara na rana agogon Najeriya na wannan Laraba.
Tuni hukumar ta nemi afuwar ƴan Najeriya, yayin da jami’anta ke kokarin maido da lantarkin.
Wannan shine karo na 12 da Najeriya ke fadawa cikin duhu na ƙasa baki ɗaya sakamakon lalacewar cibibiyon samar da wutan lantarki tun daga farkon wannan shekara ta 2024 kawo yanzu.
Lamarin da masana da ƴan kasar ke cewa ya na janyo babbar asara musamman ga 'yan kasuwa wadanda suka dogara wutan lantarki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI