Gwamnatin ta daskarar da asusun ne bayan umarnin Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja.
Sai dai a zantawarsa da RFI Hausa, Deji Adeyanju, ɗaya daga cikin jagororin zanga-zangar, ya musanta zargin mallakar wani asusu, yana mai ɗiga ayar tambaya kan yadda masu gwagwarmayar neman ƴanci za su iya mallakar maƙuɗen kuɗaɗe irin wannan.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren muryar Adeyanju.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ce ta shigar da kara a gaban kotun ta Abuja tare da neman kotun da ta ɗauki matakin rufe asusun.
Sai dai hukumar ta EFCC ba ta bayar da bayanan mutanen da ta ce sune mamallaka asusun na Crypto ba, amma ta yi amanna cewa, asusun na waɗanda suka ɗauki nauyin zanga-zangar kawo ƙarshen gurbataccen shugabanci a Najeriya ne.
Ƴan Najeriya dai sun ware kwanaki 10 da suka gudanar da zanga-zanga a cikinsu, inda suka nuna ɓacin ransu kan halin tsadar rayuwa da ƙasar ta tsinci kanta a ciki.
Masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnati da ta maido da tallafin man fetur da ta janye tare da gaggauta ɗaukar matakan sauƙaƙa wa talakawa matsin da yake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI