A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar a ranar Asabar, gwamnatin ta jajantawa Nijar kan lamarin, amma ta yi watsi da zargin taka rawa a ciki.
Ma'aikatar ta ce ƙungiyar ta'addancin ba ta samu wani tallafi daga gwamnatin Najeriya ko jami'an tsaronta ba wajen kai hari kan bututun mai da ke garin Gaya na yankin Dosso a Nijar.
Ma'aikatar ta jaddada aniyar ƙasar na yaƙi da ta'addanci tare da bayyana cewa ba ta lamunci ko goyon bayan ayyukan ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba.
“Gwamnati ta sanar da cewa masu aikata laifin ba su da goyon baya ko taimako daga hukumomin Najeriya, hasalima gwamnatin Najeriya ta jajirce wajen yaƙi da ta’addanci kuma ba za ta lamunci ko tallafa wa ayyukan irin wadannan ƙungiyoyi ba”
Sojojin Faransa
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta kuma yi watsi da zargin kasancewar sojojin Faransa a arewacin Najeriya da nufin kawo cikas ga gwamnatin Nijar.
Ta bayyana wadannan zarge-zargen a matsayin marasa tushe sannan ta bukaci jama'a da su yi watsi da su.
"Dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa a ko da yaushe tana da kyau, da kuma mutunta juna, amma babu batun tsoma baki kan harkokin cikin gida kowane bangare.
Har ila yau, ta ce, Najeriya za ta ci gaba da binciko duk wata hanya ta zaman lafiya don ci gaba da kyautata dangantakarta da Jamhuriyar Nijar domin amfanin al'ummomin ƙasashen biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI