Najeriya ta koma ta 140 daga 145 a sahun ƙasashe mafiya rashawa

Najeriya ta koma ta 140 daga 145 a sahun ƙasashe mafiya rashawa

Wannan alƙaluma na nuna cewa har yanzu Najeriyar na sahun ƙasashe ƴan gaba-gaba a fannin na cin hanci da rashawa, wanda ke da nasaba da gazawar mahukunta wajen tafiyar da jagoranci a fayyace da kuma tsare-tsaren da suka kamata.

Alƙaluman na CPI na duba yanayin cin hanci da rashawa a ƙasashen 180 daga maki sufuri zuwa ɗari ta yadda ake jerasu mataki-mataki bisa ga yawan cin hanci ko rashawar da al’ummar ƙasar ke gani ta kowanne fanni ko kuma salon tafiyar da gwamnati kama daga karkatar da kuɗaɗe ko almundahanarsu.

Wani sako da Transparency International ta wallafa a shafinta na X da safiyar yau Talata ta ruwaito shugabar ƙungiyar François Valérian na bayyana cin hanci da rashawa a matsayin mummunar matsala mai haɗarin gaske ga duniya.

Transparency International ta ce, duk da cewa wasu ƙasashe sun yi hoɓɓasa wajen murmurewa daga matsalolin na cin hanci da Rashawa amma har yanzu wasu na cigaba da ganin ta’azzarar matsalar.

Ƙungiyar ta ce daga shekarar 2012 akwai ƙasashe 32 cikin 180 da suka yi ƙoƙarin rage matsalar ta cin hanci da rashawa kodayake 148 daga ciki ko dai suna inda suke ko kuma matsalar ta ta’azzara.

Transparency International ta ce har yanzu ƙasashe 43 basu sauya daga matakin da suke tsawon shekaru ba.

A cewar ƙungiyar akwai biliyoyin mutane da ke rayuwa a ƙasashen da rashawa ke ci gaba da illata rayukan jama’a a wani yanayi da take haƙƙin ɗan adam ke kaiwa ƙololuwa a irin ƙasashen.

François Valérian ya buƙaci ƙasashe su miƙe tsaye wajen yaƙar matsalar ta rashawa wadda ya ce babbar barazana ce ga ci gaban demokraɗiyya da taɓarɓarewar tsaro baya ga ta’azzara take haƙƙin ɗan adam.

A shekarar 2019 Najeriya ta koma ta 146 bayan samun maki 26 yayinda ta koma ta 154 a 2021 bayan samun maki 24, inda ta koma ta 145 a 2023 bayan samun maki 25 gabanin komawa ta 140 a bana bayan samun maki 26.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)