
Duk da wannan kokari daga hukumomin na Najeriya a bangaren da ya shafi harkokin tsaro, an kashe akalla ‘yan Najeriya 5,801 a hare-haren ta’addanci, sannan an sace ‘yan kasar 4,348 a cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2024.
Majiyoyi a kjasar na nuni cewa an kashe mutane 2,223 a yankin Arewa maso Gabas, wanda ke wakiltar kashi 33 cikin 100 na al’amuran, inda aka kashe mutane 1,609 tare da yin garkuwa da 614 a kananan hukumomi 88.
Shin akwai wata nasara da aka samu a bangaren tsaro a kasar?
Dr. Yahuza Getso mai sharhi ne akan lamuran tsaro a Najeriya, ya yi mana tsokaci akai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI