Najeriya ta karɓi alluran rigakafin zazzaɓin cizon sauro guda dubu 800

Najeriya ta karɓi alluran rigakafin zazzaɓin cizon sauro guda dubu 800

Da ya ke karɓar rigakafin a Abuja, babban birnin ƙasar,  ministan lafiya da jin dadin al’umma, Farfesa Ali Pate ya ce za  a fara wannan rigakafi ne a jihohin Bayelsa da Kebbi, inda aka fi samun masu kamuwa da wannan cuta ta malaria.

Farfesa Pate ya ce za a  fara yi wa masu rauni daga cikin al’umma ne wannan rigakafi, wato yara ƙanana da mata masu juna  biyu da zummar inganta lafiyarsu.

Ministan, wanda ya buƙaci iyaye su ba da ƴaƴansu a yi musu wannan rigakafi, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai su taimaka wajen yaɗa bayanai a game da rashin illa da ingancin rigakafin.

Abokan hulɗar Najeriya  a game da wannan rigakafi,  Gavi, UNICEF, WHO da USAID sun jinjina wa ƙasar a game da matakan da ta ke ɗauka a kan cutar malaria, kana su ka tabbatar da ingancin rigakafin.

Rigakafin, wanda ake buƙatar a  bayar da shi sau hudu, za a sanya shi a jadawalin rigakafin da aka saba bai wa yara ƙanana ne  Najeriya, inda za a rika bai wa yara yan ƙasa da shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)