Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi duba kan yawan katsewar lantarki a ƙasar

Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi duba kan yawan katsewar lantarki a ƙasar

Kwamitin da ministan lantarki na ƙasar Adebayo Adelabu ya kafa ya ƙushi mutum 6, inda za su tattauna don kawo mafita kan yadda za’a magance wannan matsala.

Mai bawa ministan lantarki shawara kan kafafen yaɗa labarai Bolaji Tunji ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Waɗanda aka naɗa a kwamitin sun haɗa da babbar daraktar hukumar lura da manyan turakun lantarki mai zaman kanta Nafisat Ali a matsayin shugaba da Dr. Chidi Ike kwamishinan  a hukumar kula da lantarki a mstayin mamba da Injiniya Ishola shugaban cibiyar sanya ido kan yadda ake rarraba lantarki a ƙasar.

Sauran sune Emmanuel Nosike daractan lura da rarraba lantarki a ma’aikatar wuta ta Najeriya da Ali Sharifai da kwararran mai bawa ministan lantarki shawara Adebayo Olowoniyi.

Sanarwar ta ce kwamitin zai gabatar da rahotonsa daga yanzu zuwa ranar 1 ga watan Nuwambar 2024.

Sanarwar ta ƙara da cewa wata tawagar ƙwararru ta fara bincike kan matsalar da ta shafi manyan turakun lantarkin ƙasar domin  bayar da shawara kan yadda za’a magance faruwar hakan a nan gaba.

Ministan ya kuma gayyaci shugabannnin hukumomin hukumar kula da lantarki Najeriya da kuma na hukumar rarraba lantarki domin tattaunawar gaggawa da nufin shawo kan matslar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)