Ministan harkokin Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ne ya nuna buƙatar ganin Najeriya ta kasance cikakkiyar mamba ta kwamitin sulhi na Majalisa Ɗinkin Duniya, a yayin da yake bayyana tasirin da ƙasar ke dashi wajen wakiltar nahiyar Afika a kwamitin.
Da yake jawabi a yayin wani taron tattaunawa mai taken "tasirin Afrika" a taron duba tattalin arzikin duniya da aka yi a birnin Davos na ƙasar Sweden a ranar 21 ga watan Janairun 2025, ministan ya koka ga kwamitin sulhu ta Majalisar Ɗinkin Duniya bisa rashin Afrika a cikin kwamitin, yayin da yake bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na kudurorin majalisar sun shafi batutuwa masu alaka da Afirka.
Ya kuma yi nuni da cewa, da yawa daga cikin dokokin da Majalisar ta fitar na da illa ga nahiyar ta Afirka, ciki har da dokar sare dazuzzuka, wadda ta haramta sayen amfanin gona daga yankunan da aka sare dazuka, tare da yin watsi da kamfanonin fasaha da ke kera na’urorin da ke ba da damar sare dazuka a nahiyar.
Tuggar ya ƙara da cewa, ƙarƙashin mulkin shugaban Najeriya Bola Tinubu Kasar ta samu ingantuwar lamura kuma duniya ta shaida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI