Najeriya ta baiwa kamfanin Berger wa’adin mako 1 kan aikin hanyar Abuja zuwa Kano

Najeriya ta baiwa kamfanin Berger wa’adin mako 1 kan aikin hanyar Abuja zuwa Kano

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin sabon shugaban kamfanin a Najeriya Dr Pier Lubasch, wanda ya samu rakiyar shugaban kamfanin mai barin gado a ƙasar Dr Lars Richter, a ofishinsa da ke Abuja.

Idan Berger ba zai iya yi a hakan ba, bari mu nemo wasu waɗanda za su iya kuma a kan lokaci bisa farashin da muke so. Mun sami wasiku sama da 20 daga Berger kan wannan lamari. Farashin ya tashi daga Naira biliyan 710 zuwa Naira biliyan 740 saboda wannan tsaikon da aka samu, kuma idan aka ci gaba da haka, zai zame wa ma’aikatar mu matsala.

Wannan mataki da Umahi ya ɗauka, ya biyo bayan barazanar da a baya ya yi na kwace kwangilar aikin hanyar daga hannun kamfanin da gwamnatin baya ta Muhammadu Buhari ta bayar a shekarar 2019.

Tuni dai aka kammala aikin hanyar daga Kaduna zuwa Zaria kuma ana dab da kammala aikin Zaria zuwa Kano, sai dai aikin daga Abuja zuwa Kaduna ne ke tafiyar hawainiya domin kashi 27 ne kadai kamfanin ya yi a cikin shekaru 6.

A wajen wani taro da ministan ya halarta a makon jiya, ya zargi kamfanin na Julius Berger da sanya siyasa cikin aikin domin zubar da kimar gwamnati mai ci.

A yayin taron da ya yi da shugabannin kamfanin, ya nuna damuwarsa kan yadda kamfanin ke jan ƙafa wajen kama aiki gadan-gadan, matakin da ya ce ya jefa masu bin hanyar cikin garari, duk kuwa da yadda majalisar zartawa ta ƙasar ta amince da fidda kuɗin aikin.

A jawabinsa, sabon shugaban kamfanin na Julius Berger a Najeriya Dr Pier Lubasch, ya yi alkawarin duba lamarin tare da ɗaukar matakan da suka kamata don kaucewa wani ɓata lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)