Najeriya: NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki muddun aka tsare shugabanta

Najeriya: NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki muddun aka tsare shugabanta

Ƙungiyar ta yanke wannan shawarar ne a wani taron gaggawa da jagororinta suka gudanar ranar Talata a Abuja, inda ta umurci dukkan rassanta na jihohi da masu ruwa da tsaki da su hada kai da ma’aikata domin gudanar da yajin aiki na sai baba ta gani muddun wani abu ya faru da shugaban NLC, Joe Ajaero, wanda ƴan sanda su ka gayyata.

Ƴan sanda sun gayyaci Ajaero domin amsa tambayoyi kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci.

Gayyatar da ke zuwa makonni bayan da ƴan sanda suka kai samame sakatariyar NLC ta ƙasa a Abuja.

Sufeto-Janar na ƴan sandan ƙasar Kayode Egbetokun, yayin da ya ke ƙarin haske kan samamen, ya ce  ƴan sandan na bin sawun ɗaya daga cikin ƴan ta’addan da suka kitsa rikicin Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)