Najeriya na tattaunawa da ƴan kasuwa don samar da daidaitaccen farashi

Najeriya na tattaunawa da ƴan kasuwa don samar da daidaitaccen farashi

Shugaban hukumar ta FCCPC Mr Tunji Bello a jawabin da ya gabatar gaban ƙungiyoyin ƴan kasuwar da ke hada-hadar rarraba kaya a Najeriyar, ya bayyana takaicinsa da yanayin yadda farashin kayan ke hauhawa ba tare da wani dalili ba, musamman kayakin da ake sarrafawa a cikin gida.

Matakin hukumar na zuwa a dai dai lokacin da wani rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ke cewa farashin kayayyaki musamman ɓangaren abinci ya yi matuƙar hauhawa a watan Yunin shekarar nan da kashi 34.2 cikin 100.

Hukumar ta ce wannan adadi ya ƙaru ne matuƙa daga hauhawar kashi 22.8 cikin 100 da al’ummar Najeriyar suka gani a watan Yunin shekarar 2023.

Tuni dai masana suka yi maraba da wannan mataki na FCCPC lura da cewa tsawon lokaci ana kiraye-kirayen ganin mahukuntan na Najeriya sun ɗauki matakin aiwatar da dokar da za ta riƙa daidaita farashi a ƙasar.

Yanzu haka dai FCCPC na ci gaba da tattauna masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin ƴan kasuwa da masu hada-hadar rarraba kayaki a sassan Najeriya don lalubo hanyoyin magance matsalar ta hauhawar farashi da kuma daidaita farashin don zamowa na bai ɗaya.

Baya ga tsadar rayuwa da al’ummar Najeriyar ke fama da shi rashin tsayayyen farashi kan kayaki musamman na abin na matsayin babban ƙalubalen da ke addabar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)