Najeriya na shirin kwashe ƴan ƙasarta da ke Lebanon saboda ɓarkewar rikici

Najeriya na shirin kwashe ƴan ƙasarta da ke Lebanon saboda ɓarkewar rikici

Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan ta shafinsa na X a ranar Talata, in da ya bukaci ƴan Najeriya mazauna ƙasar Lebanon da su ziyarci ofishin jakadan Najeriya domin gabatar da bayanansu.

Rahotanni na cewa akwai ƴan Najeriya sama da dubu biyar da ke zaune a ƙasar Lebanon.

A ranar Talata Iran ta harba makami mai linzami kimanin 200 cikin Isra'ila a matsayin martani kan kisan shugabannin Hezbollah.

Kasashen biyu sun yi musayar barazana bayan harba makami mai linzami da Tehran ta yi.

Firamistan Isra'ila, Benjamin Netantahu, ya yi alkawarin cewa ƙasarsa za ta mayar da martani mai tsanani.

A nasu bangaren, kasashen China da Saudiyya sun yi kira da a kwantar da hankula kan halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, kana sun bukaci bangarorin da su koma tattaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)