Najeriya na gab da fara haƙar gangar ɗanyen mai miliyan 3 kowacce rana- NNPC

A cewar NNPCL ta bakin jami’in yaɗa labaranta Olufesi Soneye iya haƙar ganga miliyan 3 na ɗanyen man fetur abu mai yiwuwa ne a Najeriyar matuƙar za a samu cikakken goyon baya daga ɓangarorin masu ruwa da tsaki kama daga jami’an tsaro da gwamnatin ƙasar dama kamfanonin mai masu zaman kansu.

A jawabinsa gaban wani taron masu ruwa da tsaki na a harkar man da ya gudana a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, Soneye ya ce lura da nasarorin da aka samu bayan matakin gwamnati na tsaurara matakan tsaro da a baya-bayan nan ko shakka babu idan har aka sake haɗa ƙarfi waje guda za a iya cimma haƙo gangar miliyan 3.

A baya-bayan nan ne dai kamfanin na NNPCL ya ƙara yawan man da ya ke haƙowa a kowacce rana daga ganga miliyan 1 da dubu 400 zuwa ganga miliyan 1 da dubu 700 sakamakon daƙile ayyukan masu fasa bututun mai.

Ayyukan masu fasa bututun man da masu fasa ƙwaurin ɗanyen man da ya ta'azzara a baya shi ne ya kassara yanayin man da Najeriyar ke fitarwa ƙetare don tacewa, sai dai cikin watanni baya-bayan nan haɗin gwaiwar jami'an tsaron sun yi nasarar kame ɓatagari da dama baya ga daƙile ayyukan masu fasa bututun wanda ya taimaka wajen ƙaruwar man da ƙasar ke iya haƙowa.

A cewar jami'in na NNPCL idan har aka kange barazanar ɓatagarin da ke hana rawar gaban hantsi a lamarin na haƙar ɗanyen mai ko shakka babu abu ne mai sauki akai ga iya haƙar ganga miliyan 3 ta ɗanyen man a mahaƙun Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)