Najeriya: Masu zanga-zangar yunwa za su biya naira miliyan 10 a kan beli

Najeriya: Masu zanga-zangar yunwa za su biya naira miliyan 10 a kan beli

Mai shari’a Emeka Nwite  ya sanya belin a kan kudi da ya kai naira miliyan 10 a kan kowannen su, inda za su kuma kawo mai tsaya musu, wanda dole ya kasance yana da gida a birnin  Abuja  da ya kai darajar kuɗin belin. Kana dole masu tsaya musun su miƙa fasfunansu ga hukuma.

Mutanen da aka gurfanar da su gaban kotun a ranar 2 ga watan Satumba, sun musanta aikata laifuka 6 da ake zargin su da aiktawa da suka haɗa da shirya yaƙi, da yunkurin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Ko da ya ke lauyoyin su sun gabatar da bayanin cewa shaidun da gwamnati ta gabatar ba su nuna zargin cin amanar ƙasa ba.

An kuma zargi mutanen da kai wa jami’an ƴan sanda, ƙona ofishin ƴan sanda da lalata sauran kadarori.

Lauyan waɗanda ake zargi, Abubakar Marshal, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta sake nazari a kan zarge-zargen, yana mai nuni da cewa ƙarin wasu masu zanga-zanga 49 na tsare a gidan yarin Kujea ƙarƙashin umurnin kotu.

An ɗage shari’ar har sai ranar 27 ga watan Satumban nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)