Rahotanni sun ce ɗan kasuwan da aka harben har lahira, yana daga cikin masu kalllon gwabzawar da ake yi ne, wanda ɓcin rana ta sa harsashi ya same shi a ƙirji a lokacin da ya ke ƙoƙarin barin wurin da gudu a yankin Wuse Zone 6.
Wani ganau ya ce a lokacin da aka garzaya da mutumin asibitin Wuse Zone 2, an tarar cewa sashen kula da ,waɗanda ke namn taimakon gaggawa ya cika da jami’an ƴan sanda da ake wa magani, lamarin da ya sa aka yanke shawarar wucewa da shi wani asibitin a Maitama, amma ya mutu a kan hanya.
Ƴan Shi’an su na cikin wani tattaki ne na zuwan kwana 40 bayan bikin Ashura wannan rikici ya ɓarke.
Majiyoyi sun ce masu tattakin sun yi ta jifan ƴan sanda da duwatsu, kuma su ci ƙarfin ƴan sandan har suka ƙwace bindigoginsu, lamarinnda ya sa jami’an su ka ranta a na kare.
Da ta ke mayar da martani a kan lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh ta ce tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce masu tattaki sun afka wa ƴan sanda ba gaira ba dalili, lamarin da ya tada wannan rikici, tana mai tabbbatar da cewa an kashe ƴn sanda biyu, aka jikkata da dama aka kuma sumar da guda biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI