Najeriya da India sun sun sake farfaɗo da alaƙarsu ta tsaro da tattalin arziki

Najeriya da India sun sun sake farfaɗo da alaƙarsu ta tsaro da tattalin arziki

Hakan dai ya biyo bayan ziyarar da firaministan India Narendra Modi ya kai ƙasar da ke yammacin Afirka, bayan gayyatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa.

A ganawar ta jiya Lahadi da shugabannin biyu suka yi a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, tattaunawarsu ta fi mai da hankali ne ɓangaren tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da kuma fannin samar da wadatatcen abinci.

Ƙasashen biyu dai sun cimma matsaya wajen hada kai don yaki da matsalar tsaro a mashigar Tekun Guinea, inda suka sha alwashin yaƙi da ƴan fashin teku.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da fira ministan India Modi. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da fira ministan India Modi. © Nigerian presidency

Wannan kuwa na zuwa ne a dai-dai lokacin da dukkanin ƙasashen biyu ke neman ƙujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A ɓangaren tattalin arziki kuwa, ofishin firaministan India ya ce ƙasar na da sama da kamfani dari 2 a Najeriya, kuma sun zuba jarin sama da dala biliyan 27 a ƙasar.

Najeriya dai na neman ƙarin kamfanonin masu zuba jari daga India, da ƙarin hanyoyin samun rance da za ta yi amfani da su wajen bunƙasa tattalin arzikinta.

Haka nan India ta sha alwashin marawa yunkurin da Najeriya ke yi baya, wajen ganin ta shiga ƙungiyar G20 da kuma BRICS.

Ziyarar ta ƙarshen mako da Narendra Modi ya kai Najeriya dai, ita ce ta farko cikin shekaru 17, da wani firaministan India ya kai ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)