Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan amincewa da katafaren aikin ne yayin ziyarar kwanaki uku da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai ƙasar ta Equatorial Guinea inda ya gana da shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
Yayain ziyarar shugabannin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwan da suka haɗa da matsalolin tsaro, ƙarancin abinci, da kuma samar da ayyukan yi.
Kafin yarjejeniyar da Najeriya ta ƙulla da Equatorial Guinea, a shekarar 2016 giwar nahiyar Afirkan ta fara ƙulla yarjejeniya da Morocco kan shimfiɗa bututun man da za su riƙa sayar wa nahiyar Turai.
Ana sa ran aikin da ƙungiyar ECOWAS ke marawa baya, zai laƙume dalar Amurka biliyan 25, bayan kammala shimfiɗa shi, kuma bututun man zai ke samarwa da Turai iskar gas ɗin da yawanta ya kai ma’aunin cubic biliyan 30 a duk shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI