
A ƙarshen makon da ya gabata ne aka tabbatar da wannan yarjejeniya a hukumance a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom a tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin APPL Hydrogen Limited (AHL), da LONGi Green Energy Technology Company Limited na ƙasar China.
Za a gudanar da wannan aiki ne yankin da aka sakar wa yan kasuwa mara su gudanar da sabgoginsu, wato Liberty Free Trade Zone da ke garin Atabrikang a ƙaraamar hukumar Ibeno ta jihar Akwa Ibom.
Kamfanin LONGi, wanda ke kan gaba a hakar sauyawa zuwa amfani da makamashi mara gurɓata muhalli a duniya, da AHL na Najeriya, wanda ya ƙware wajen samar da makamashi da ba ya illata muhalli ne za su yi haɗaka don tafiyar da aikin, kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da aka yi.
Da yake jawabi a yayin rattaba hannu a yarjejeniyar, ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji ya jaddada mahimmancin shirin a koƙarin da Najeriya ke yi wajen sauyawa zuwa amgfani da makamashin da ba ya illa ga muhalli.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI