Wakili ya shaidawa RFI Hausa cewar matsalar tsaron Najeriya ba ta 'yan sanda ba ne, sai dai na yadda gwamnati bata bada isassun kudin aiki da kuma kayan aikin da ake bukata wajen ganin jami'an sun gudanar da aikin su ba tare da fuskantar matsala ba.
Tsohon kwamishinan yace a koda yaushe 'yan sandan Najeriya suka je aiki kasashen ketare a karkashin majalisar dinkin duniya su suke zuwa na farko saboda kwarewar su da kuma kayan aikin da ake wadata su da shi, amma kuma a gida basa samun irin wadannan kayan aikin da suke bukata.
Wakili yace abin takaici yanzu tashoshin 'yan sanda da dama basu da motar aiki, kuma sau tari inda ka ga motar za ka ga babu kudin mai, yayin da kuma makaman da jami'an ke aiki da shi tsofaffi ne, sabanin wadanda masu aikata laifuffuka ke amfani da su.
Tsohon kwamishinan ya ce suna jira su ga irin dokar da za'ayi wajen samar da 'yan sanda a daidai lokacin da yake bayyana fargabar cewar tabbas za'a samu arangama tsakanin su da na tarayya wajen gudanar da aiki.
Tsohon jami'in yace rashin amfani da dokokin kasa sune matsalolin da suka yiwa harkokin mulki da na tsaro dabaibayi, kuma suka haifar da matsalolin da yanzu haka ake fuskanta a jihohin Rivers da Kano.
Wakili yace mudin za'ayi amfani da doka da oda, to babu dalilin da zai sa a bukaci kafa irin wadannan 'yan sanda na jihohi wadanda ka iya haifar da matsaloli musamman a karkashin jagorancin 'yan siyasa.
Idan dai ba'a manta ba, taron Majalisar tattalin arzikin Najeriya da ya kunshi gwamnoni 36 da kuma mataimakin shugaban kasa ya bayyana samun hadin kai dangane da shirin kafa 'yan sandan jihohin wanda ya bayyana cewar ana saran kammala tattaunawa a kai a farkon shekara mai zuwa.
'Yan Najeriya da dama cikin su harda masana harkar tsaro na bayyana fargaba a kan yadda wadannan jami'ai za su yi aiki a jihohi, ganin yadda wasu gwamnonin jihohin ke mulkin kama karya musamman wajen murkushe masu adawa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI