Ɗaya daga cikin waɗanda su ka tsere daga Allawa ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa a sun tura wasu mutane gida don tantance ko za su iya komawa don ci gaba da noma, amma sai suka gamu da ƴan ta’adda a cikin gidajensu, kuma har sun nome gonakin nasu.
Ya ce ƴan ta’addan sun kuma yi amfani da takin da suka sayo kafin su arce daga garin, kana suka banka wa wasu daga cikin gidajen wuta.
A watan Afrilun wannan shekarar ne rahotanni suka karaɗe kafafen yaɗa labaran Najeriya a game da tserewar al’ummar Allawa daga garin nasu, sakamakon janye sojojin da ke ba su tsaro da aka yi daga yankin.
A wannan lokacin, mahukuntan jihar Neja sun tabbatar da janye sojojin, amma sun ce ba su da wani iko a kan hakan, su na mai cewa lamari ne da ya shafi rundunar sojin ƙasar, waɗanda suka ce su na janyewa ne don sake ɗamara da dabara.
A halin da ake ciki, mazauna wannan gari na Allawa sun yi kira ga gwamnatin jihar data tarayya da zu ɗauke ƙwararan matakan kawar da waɗannan ƴan ta’adda daga garin nasu, domin su samu ssu koma gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI