Najeriya: Al'ummar Jihar Jigawa sun ki fita zaben ƙananan hukumomi

Najeriya: Al'ummar Jihar Jigawa sun ki fita zaben ƙananan hukumomi

A zagayen da waƙilinmu na Jigawa ya yi a akasarin mazaɓun jihar,  ya lura cewa al’umma na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda su ka saba, a yayin da malaman zaɓe su ke jira masu zaɓen su fito.

 Wasu da aka tattauna da su a yayin zagayen, sun nuna cewa sun manta cewa a wannan ranar ce za a gudanar da zaɓen, kamar yadda wani matashi da muka zanta da shi mai suna Hamisu Adamu, wanda ya ce, "Aw wai dama yau ake zaɓen? Ni ai kwata-kwata na manta ma yanzu ka ganni shago zan tafi don ya fi mun mutunci, tun da ko ba komai zan samu na cefane, amma idan na tafi zaɓe wanda na zaɓa ba shi za su ba wa ba".

Ya ce, "wannan zaɓen da shi da naɗi duk ɗaya ne, don haka babu bukatar bata lokaci kawai, kowa ya yi abin da zai fishe shi".

Shi ma Muhammad Zulyadaini, ya ce bai ga amfanin zuwa zaɓen da babu abokan hamayya ba.

"Ni ka gan ni ma wallahi yanzu daga filin kwallo nake, ina sane an ce yau za a yi zaɓe, amma ina amfanin ɓata lokaci? To kai dan jarida na tambaye ka ma, duk inda ka zaga ka ga inda wasu suka fito zaɓen? Ai wannan zaɓen kawai suna ne", ya ƙarƙare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)