Fafesan Ya kuma bayyana cewa da yawa daga cikin shugabannin Najeriya na ci gaba da kaurace wa batun tattaunawa game da samar da ingantattun sauye-sauye ko kuma hsirya sabon kundin tsarin Mulki da ka iya taimakawa ƙasar.
Moghalu ya yi wannan magana ce a yayin wata ganawa da ta gudana ta yanar nuna damuwarsa dangane da abin da ya shafi Jagoranci a Afirka, wanda masanin tarihi, Farfesa Toyin Falola ya nuna damuwarsa akai.
Sai dai wani masanin tattalin arzikin kuma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN sannan ɗan tsohon takarar shugaban kasa ya bayyana cewa dole ne a samu daidaito a tsakanin kabilu mabambanta a ƙasar domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, kafin a samu nasarar ci gaban da aka sanya a gaba.
A yayin da yake amsa tambayoyi game da zaben 2027 da kuma bukatar samar da sabon kundin tsarin mulki, ya ce, “Ina ganin a ko da yaushe matsayata a fili take cewa Najeriya na bukatar sabon kundin tsarin mulki, idan har tana bukaƙar tsayawa kan ƙafafunta rara da kuma samar da mafita game da halin da ta ke ciki na matsalar tattalin arziki na siyasa.
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin na CBN ya ƙara da cewa "Muna buƙatar komawa kan kan teburin shawara, tare da duba maganar Walter Lippmann na Amurka, 'yan kabilun na bukatar su zauna wajen duba muhimmancin Najeria a garesu, domin fahimtar irin rawar da ta kamata su taka wajen ci gaban kasnu da kansu
Ya kuma da cewa “Idan aka samu kyakkyawar matsaya, za a iya samun kwanciyar hankali da karin zaman lafiya kuma da zarar abin ya faru lamura zasu inganta."
Ya bayyana cewa da yawa daga cikin shugabannin siyasa na ci gaba da kau da kai daga tattaunawa game da ɗorewar ƙasar, da kuma samun sabon kundin tsarin mulki saboda fafutukar tafiyar da lamuran ƙasar ta yadda komai zai gudana cikin kwanciyar hankali da yalwatar tattalin arziki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI