
Hukumar NAFDAC ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, inda ta ce an gano magungunan na jabu a cikin wasu gine-gine a garin Umumeje, a karamar hukumar Osisioma Ngwa ta jihar.
Hukumar ta ce harabar gine-ginen na kusa da kasuwar Ariaria da ke garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar.
Hukumar NAFDAC ta ce an gano ma’ajiyar ne a lokacin da ta kai samame wurin tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na hadin gwiwa a wani bangare na yaki da jabun magunguna da gwamnatin tarayya ke yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI