NAFDAC na ci gaba da farautar masu sarrafa jabun magunguna a kudancin Najeriya

A farkon watan Fabrairun nan ne, NAFDAC ta ce, jami’anta sun gano wani katafaren wurin hada-hadar sayar da magunguna da ya kasance cibiyar sake gyarawa da sabunta magungunan da suka lalace don sake siyarwa da su a jihar Abia.

Hukumar ta ce harabar gine-ginen na kusa da kasuwar Ariaria da ke garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar.

Hukumar NAFDAC ta ce an gano ma’ajiyar ne a lokacin da ta kai samame wurin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na haɗin gwiwa a wani bangare na yaƙi da jabun magunguna da gwamnatin tarayya ke yi.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Murtala Adamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)