Tun a watan Yuni aka rufe cibiyoyin kananan hukumonin , biyo bayan takun sakar siyasa tsakanin Gwamna Fubara da tsohon amininsa na siyasa, minibabban birnin tarayya Abuja, Minista Nyesom Wike.
Rufewar ta tilasta wa shugabannin riko da Fubara ya nada su yi aiki daga wasu wurare.
Duk da kokarin da Wike ya yi na hana su, an gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 5 ga Oktoba. Da kuma a jiya litinin sabbin shugabannin sun shiga ofishin su domin kama aiki.
Jihar Rivers na kan gaba cikin jihohin da ke da tsananin zafin siyayar adawa a tarayyar Najeriya, ga kuma rashin jituwa dake tsakanin gwamna Fubara da Tsohon gwamna Wike.
Masana a bangaren siyasa da ‘yan siyasar dai na kallon gwamnatin tarayyar kasar nada gagarumar rawar takawa hakan batun tun kafin ya kai ga haka sai da ta kawar da kai.
Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar dai ta bisa umarnin babban sefeton ‘yan sanda Najeriya ta karbi cibiyoyin kananan hukumomin a baya sai dai janyewarsu domin bada damar gudanar da aikin dimokradiyya ya baiwa ‘yan tada zaune tsaye damar sanya wutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI