Rahotanni daga yankin na nuni cewa lamarin ya faru ne yayin da wata tankar mai dauke da PMS ta yi karo da wata motar tirela da ke dauke da matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano da ke kan hanyar zuwa Legas.
Wasu motocin biyu kazzalika sun kuma kone yan lokuta bayan faruwar lamarin.
Motar kai agajin gaggawa a Suleja REUTERS/Afolabi SotundeTa bakin babban jami’in kula da hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja, Alhaji Abdullahi Baba Arah, jami’in ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa, hukumar ba da agajin gaggawa ta NSEMA ta amsa kiran bayan aukuwar hadarin, inda ya ce an gano gawarwaki kusan mutane 30 daga cikin motar.
Alhaji Abdullahi Baba Arah ya ce har yanzu jami’an hukumar na nan a wurin da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike tare da kuma agajin da ya dace ga wandada suka samu rauni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI