Mutane kusan 20 ne suka mutu bayan da injin kwale-kwalen da suke ciki ya kama da wuta

Mutane kusan 20 ne suka mutu bayan da injin kwale-kwalen da suke ciki ya kama da wuta

"Jirgin ruwan wani babban jirgin ruwa ne mai dauke da mutane sama da 100, akasarin su 'yan kasuwa,kamar dai yada Adebiyi Babatunde Razaq na hukumar NEMA ya tabbatar,jami’in ya karasa da cewa hadarin ya faru ne "da safiyar Laraba",bayan ya taso ne daga garin Ekeni kafin injinsa ya kama da wuta a unguwar Ezetu I da ke gabar tekun Atlantika da misalin karfe 3 na rana, a yayin da yake tafiya zuwa Swali a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Yankunan Neja Delta Yankunan Neja Delta Yasuyoshi CHIBA / AFP

 A wata sanarwa da hukumar kula da kuma sa ido don kiyaye hadura saman ruwa ta Najeriya ta fitar ta ce hatsarin ya faru ne bayan da injin wannan jirgi yak ama da wuta.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance kan musabbabin hatsarin, amma gwamnan jihar Duoye Diri, ya yi kira da a bi ka’idojin tsaro.

Wani jirgin dakon Mai da aka cinawa wuta a yankin Neja Delta Wani jirgin dakon Mai da aka cinawa wuta a yankin Neja Delta (Photo : Reuters)

Wannan yankin ya kasance wani yanki da ake yawan tafiye-tafiyen cikin jiragen ruwa a Najeriya, musamman a yankin Neja Delta da ke gabar teku.

Hatsarin da ya afku a ranar Laraba a jihar Bayelsa da ke kudancin Ijaw, shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin masifu makamancin wannan a Najeriya, inda kwale-kwale sukan nutse saboda an loda kaya fiye da kima da kuma rashin bin ka’idojin tsaro ko kuma rashin kyawun yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)