Rahotanni sun ce jami’an tsaro ne suka harbe mutane huɗun, a lokacin da suka nuna turjiya akan rushe musu gidaje da jami’an Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano KNUPDA suka yi a yankin.
Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa kimanin gidaje 40 ne hukumar ta KNUPDA ta shafa wa jan fenti, bayan zargin ginasu a filaye mallakin Jami’ar Bayero ta Kano.
Wani mazaunin yankin da abin ya shafa, ya ce a baya hukumar ta KNUPDA ta tabbatar musu cewar ba a filayen jami’ar aka yi gine-ginen ba.
Jaridar ta ce duk ƙoƙarin jin ta bakin shugaban hukumar ta KNUPDA da ta yi abin ya ci tura, sannan kuma wakilinta da ya ziyarci ofishin hukumar ya ce da dama daga cikin manyan jami’ata ba su je aiki ba, saboda fargabar abinda ka iya je ya ya dawo.
To sai dai wani jami’in KNUPDA ya shaida wa jaridar cewar ba jami’ansu ba ne suka gudanar da rusau a unguwar ba, jami’an Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ta jihar ne suka aiwatar da aikin.
Tuni wani jami’i daga Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ta jihar Kano da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da wuraren da aka gudanar da aikin rusau ɗin mallakin Jami’ar Bayero ne, kuma ya ce nan bada jimawa ba gwamnati za ta fitar da sanarwa a hukumance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI