Mutane hudu suka mutu a hadarin mota a Ebonyi wanda da ya rutsa da ‘yan NYSC

Mutane hudu suka mutu a hadarin mota a Ebonyi wanda da ya rutsa da ‘yan NYSC

 ‘Yan kungiyar sun nufi sansanin horar da masu yi wa kasa hidima na NYSC ne domin samun horo na tsawon makonni uku a lokacin da motar bas mai dauke da kujeru 14 da suke ciki ta kutsa kai cikin wata babbar motar dakon kaya.

Matasan na daga cikin mambobin kungiyar 2024 Batch C Stream 2 da aka tura domin yin hidima a Ebonyi kuma suna kan hanyarsu ta zuwa sansanin Kwalejin Permanent Orientation na MacGregor a karamar hukumar Afikpo ta jihar.

Hadarin wanda ya rutsa da wata motar bas ta Enugu North Mass Transit da suka shiga, ta kutsa kai a karkashin wata babbar motar da ke tsaye a cikin titin Okposi a karamar hukumar Ohaozara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da jikkata wasu daga cikin fasinjoji.

Rahotanni na nuni cewa fasinjojin da suka jikkata an garzaya da su asibitin Koyarwa na Jami’ar David Umahi domin yi musu magani.

Sanarwar da asibitin ta fitar ta shafinta na sada zumunta ta ce adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa hudu, ciki har da wasu jami'an hukumar yiwa kasa hidima biyu.

 Sanarwar daga likita na cewa wadanda suka tsira a halin yanzu suna samun murmurewa, kuma jami’an asibitin na da kwarin gwiwa game da yiwuwar samun cikakkiyar lafiya. Sanarwar ta ce daukar matakin gaggawa na asibitin na bayar da kulawa ga wadanda hadarin ya rutsa da su na da matukar muhimmanci wajen daidaita su. Sanarwar ta ce "Babban Daraktan asibitin, Farfesa Uzoma Agwu ne ya tabbatar da hakan, wanda ya hada dukkan ma'aikatan asibitin domin su kai dauki ga wadanda abin ya shafa, tare da tabbatar da samar da magunguna da kayayyakin da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)