Ministan kudin kasar Wale Edun ya bayyana cewar tun a watan Yunin bara suka hango cewar kudaden da suke samu daga man fetur zai ragu, saboda haka suka sake dabarar duba wasu hanyoyin samun kudade cikin su harda cire tallafin mai da wutar lantarki da inganta harkokin tara haraji ta hanyoyin zamani tare da daidaita farashin kudaden ketare.
Ministan yace suna taskance kudade sosai ta wadannan hanyoyi tare da karkata akalarsu zuwa bangarorin noma da kula da lafiya da samar da tsaro da kuma bangaren ilimi.
Mataimakin daraktan Bankin Duniya Ndiame Diop ya ce daga cikin sauye sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa, batun kara kudaden haraji na da matukar tasiri , saboda raguwar harajin zai sanya kasar dogara da karbar bashi, kamar yadad Najeriya ta biya kusan kashi 6 na kudaden da take samu a shekarar 2022 domin biyan kudin ruwan bashin da ake binta.
Gwamnatin na ci gaba da rokon jama'ar kasar da su kara hakuri da matakan da take dauka tare da alkawarin cewar nan bada dadewa ba za su ci moriyar matakan da ake dauka masu radadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI