Kalaman na IMF na zuwa ne mako guda da ya musanta cewa yana da hannu a matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man, lamarin da ƴan Najeriya ke cewa, shi ne silar jefa su cikin mawuyacin hali.
Asusun na IMF ya dage kan cewa, tsare-tsaren shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka haɗa da janye tallafin man da kuma ƙarya darajar kuɗin kasar za su taimaka matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.
IMF ɗin ya ƙara da cewa, matakan za su kawo sauƙi ga al'ummaar Najeriya da ke cikin mawuyacin hali saboda tsadar rayuwa.
A makon jiya ne, Asusun Bada Lamunin ya ce sam babu hannunsa a janye tallafin a Najeriya bayan ya yi ta shan suka daga ƴan ƙasar..
A yayin zantawa da manema labarai a birnin Washington DC na Amurka, Darektan IMF a yankin Afrika, Abebe Selassie ya bayyana matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man a matsayin batu na cikin gida.
Matakin na cikin gida ne. Ba mu da wani shiri a Najeriya. Rawar da muke takawa ta taƙaita ne kan tattaunawa a kai a kai, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe irinsu Japan ko kuma Birtaniya. Inji Selassie.
Kodayake Selassie ya bayyana cewa, matakin na gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man na da nasaba da manufofinta na dogon-zango domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya janye tallafin ne jim kaɗan da shan rantsuwar kama aiki a watan Mayun bara bayan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.
Jim kaɗan da janye tallafin ne, farashin litar mai da sauraren kayayyaki ya yi tashin goron zabbi a sassan ƙasar.
Har yanzu dai ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda ake sayar da lita mai a kan naira dubu 1,200 duk kuwa da cewa shugaba Tinubu ya karɓi ƙasar ce a lokacin da ake sayar da lita a kan naira 200.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI