Kakakin Hukumar Kula da gidajen Yari na Najeriya, Umar Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ambaliyar ruwan da ta samu asali bayan rugujewar madatsar ruwa ta Alau, ta mamaye sassa daban-daban na birnin, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan biyu da muhalla tare da hallaka wasu da dama.
Jami'in ya ce fursunonin 281sun tsare ne a lokacin da jami’an ma’aikatar tare da tallafin wasu jami’an tsaro ke ƙokarin kwashe su zuwa wani gidan yarin mafi tsaro sakamakon rushewar katangar.
Akwai bayanansu a hannun hukumomi
Hukumar ta ce, suna da cikakken bayanan ɗaukacin fursunonin da suka tsare harda hoton yatsunsu.
Malam Umar Abubakar ya ce tuni suka sake kame 7 daga cikin fursunonin da suka tsare, kuma yanzu haka suna aiki tukuru da sauran jami'an tsaro domin gano sauran wadanda suka tsaren.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI