Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya Vice Admiral Emmanuel Ogalla ne ya bada tabbacin haka a lokacin da yake kaddamar da aikin dakarunsu dake yaƙi da masu satar ɗanyan mai ƙarƙashin Operation Delta Sanity kashi na II a Fatakwal.
Ogalla ya ce wajibi ne a cika umarnin shugaban kasa Bola Tinubu domin tabbatar da haka.
A cewarsa tun lokacin da aka ƙaddamar da rundunar yaƙi da masu satar ɗanyen mai da masu fasa bututun an samu raguwar masu aikata laifuka, kuma an samu karuwar gangar ɗanyen mai da ake haƙowa daga miliyan 1 da dubu 400 zuwa miliyan 1 da dubu 800 a kowacce rana.
Babban Hafsan sojin na ruwa na Najeriya Vice Admiral Ogalla ya ce sun fara shirin tabbatar da ganin an cimma burin fitar da ganga miliyan 3 ko sama da haka a kowacce rana.
A nashi baganaren babban kwamandan sojin ruwa na Najeriya dake kula da gabashin ƙasar Rear Amiral Saheed Akinwande ya ce aikin dakarun nasu na Delta Sanity an fara shi ne a watan Janairu kuma ya kawo babban ci gaba wurin daƙile satar ɗanyen mai a kasar.
Ya ce sun samu nasarar kama mutum 315 da ake zargi da aikata laifukan satar ɗanyen mai da kuma bankaɗo matatun man fetur da aka samar ba bisa ka’ida ba guda 468.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI