Mun samu bukatar ƙirƙiro sabbin Jihohi 31 a Najeriya - Kalu

Mun samu bukatar ƙirƙiro sabbin Jihohi 31 a Najeriya - Kalu

Shugaban kwamitin, Benjamin Kalu, wanda shi ne mataimakin shugaban Majalisar wakilai, ya bayyana haka a zaman majalisar.

Kalu ya ce buƙatun sun haɗa da 6 daga Arewa ta Tsakiya, 4 daga Arewa ta Gabas, 5 daga Arewa ta Yamma, sai kuma 5 daga Kudu maso Gabas da 4 daga Yankin Kudu maso Kudu da 7 daga Kudu maso Yamma.

Ga jerin buƙatun kamar yadda Kalu ya bayyana.

- Jihar Okun daga Kogi

- Jihar Okura daga Kogi

- Jihar Confluence daga Kogi

- Jihar Benue Ala daga Benue

 - Jihar Apa daga  Benue

- Jihar FCT daga FCT

- Jihar Amana daga Adamawa

- Jihar Katagum daga Bauchi

- Jihar Savannah daga Borno

- Jihar Muri daga Taraba.

- Jihar New Kaduna daga Kaduna

- Jihar Gujarat daga Kaduna

- Jihar Tiga da Ari daga Kano

- Jihar Kainji daga Kebbi 

- Jihar Etiti da Orashi a yankin Kudu maso Gabas

- Jihar Adada daga Enugu

- Jihar Orlu da Aba daga Kudu maso Gabas

- Jihar Ogoja daga Cross River

- Jihar Warri daga Delta

- Jihar Ori da Obolo daga Rivers

- Jihar Torumbe daga Ondo;

- Jihar Ibadan daga Oyo

- Jihar Lagoon daga Lagos

- Jihar Ijebu daga Ogun

- Jihar Oke Ogun/Ijesha daga Oyo/Ogun/Osun

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)