Mun kashe kwamandojin ƴan ta'adda dari 3 a cikin watanni 16 - Tinubu

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da yi yiwa al’ummar ƙasar, na cika shekaru 64 da samun ƴancin kai.

Tinubu ya bayyana cewar kafin zuwan gwamnatinsa watanni 16 da suka gabata, Najeriya na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da kuma na tsaro, inda ya ce sauya tsarin yadda ake tunkarar matsalar da suka yi ne ya sanya ake samu nasarar yaki da ta’addanci da aka yi.

Ya tabbatar da cewar gwamnatinsa ce mafi sauri wajen kashe manyan kwamandojin Boko Haram da kuma ƴan bindiga a ƙasar, domin a cewarsa an samu nasarar kashe sama da dari 3.

A cikin sama da shekara guda na gwamnatinmu, ta kawar da kwamandojin Boko Haram da ƴan bindiga da dama a cikin ƙanƙanin lokaci fiye da kowane lokaci. A ƙidayar karshe da aka yi, sama da kwamandojin Boko Haram da na ƴan bindiga dari 3 sojojinmu suka samu nasarar kashewa a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, da ma wasu sassan ƙasar nan.

Shugaba Tinubu ya ce ya  na cike da farin cikin yadda aka samu nasarar dawo da zaman lafiya a wasu garuruwa da ke yankin Arewacin ƙasar, lamarin da ya ce ya sanya dubban mutane komawa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)